Taswirar kasashen da ke da ofisoshin diflomasiyya na TurkiyyaHaɗin gwiwa tsakanin Amurka da Turkiyya a ma'aikatar harkokin waje
Ma'aikatar Harkokin Waje ( Turkish: Dışişleri Bakanlığı ) ma'aikatar gwamnati ce ta Jamhuriyar Turkiyya, mai kula da manufofin ƙasashen waje da huldar ƙasa da ƙasa. An kafa ma'aikatar ranar 2 ga watan Mayu 1920, ayyukanta na farko shine gudanar da ayyukan diflomasiyya, bada shawarwari da yarjejeniyoyin ƙasa da kaysa, da wakilcin Jamhuriyar Turkiyya a Majalisar Dinkin Duniya.[1] Ma'aikatar tana da hedikwata a babban birnin Turkiyya na Ankara[2] kuma tana aiki fiye da ayyuka 200 a matsayin ofisoshin jakadanci, ofisoshin wakilci na din-din-din da kuma ƙaramin ofishin jakadancin, a ƙasashen waje.
ministan Turkiya ya na ganawa da ministan harkokin waje
Ya zuwa shekara ta 2021, Ma'aikatar Harkokin Wajen tana kula da ofisoshin diflomasiyya 235 a duk duniya. Mevlüt Çavuşoğlu shi ne ministan harkokin wajen Turkiyya na yanzu, wanda aka naɗa a ranar 29 ga watan Agustan shekara ta 2014.[3]
A shekara ta 1793, Sultan Selim na Uku ya kafa ofishin jakadancin Turkiyya na din-din-din a London.
Ban da ƙaramin ofishin jakadanci, Turkiyya na da wakilai 236, daga cikinsu 142 ofisoshin jakadanci ne, 12 kuma na din-din-din, 81 na ƙaramin ofishin jakadancin, biyu kuma ofisoshin kasuwanci ne. Turkiyya na da ayyuka 235 a duniya bayan ƙasashen China (276), Amurka (273), Faransa (267), Japan (247) da Rasha (242).
Daga cikin jakadun Turkiyya 236 da ke aiki a watan Maris din 2016, 37 mata ne.
Jamhuriyar Turkiyya mamba ce ta ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 26. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ce ke kula da huldar da ke tsakanin waɗannan kungiyoyi da Turkiyya.
Jerin Ƙungiyoyin Ƙasashen Duniya
Sunan Ƙungiyar Ƙasa ta Duniya
Matsayin Jamhuriyar Turkiyya
Tattaunawar Haɗin gwiwar Asiya
Memba
Tarayyar Afirka
Member mai lura
Sojojin Ruwa na Bahar Maliya
Memba
Al'ummar jihohin Latin Amurka da Caribbean
Tarukan da ba memba ba, na hudu kan taron Majalisar Dinkin Duniya
Taron kan Haɗin kai da Matakan Gina Amincewa a Asiya