Montenegro ko Monteneguro[1] ƙasa ce, da ke a nahiyar Turai. Babban birnin ƙasar Montenegro Podgoritsa ne. Montenegro tana da yawan fili kimani na kilomita arabba'i 13,812. Montenegro tana da yawan jama'a 631,219, bisa ga jimilla a shekarar 2020. Montenegro tana da iyaka da ƙasasen huɗu: Bosnia-Herzegovina a Arewa maso Yamma, Serbiya a Arewa maso Gabas, Kosovo a Gabas da Albaniya a Kudu maso Gabas. Montenegro ta samu yancin kanta a shekara ta 2006 (akwai ƙasar Montenegro mai mulkin kai daga shekara ta 1852 zuwa shekara ta 1918 ; daga shekara ta 1918 zuwa shekara ta 2006, Montenegro yanki ce a cikin tsohon ƙasar Yugoslaviya, san nan Serbiya).