Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook
Jump to content

Akushi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
hoton abubuwan da akayi da ice irinsu Akushi

Akushi wani mazubin abinci ne wanda ake amfani da shi wajen zuba abinci dafaffe. Musamman a zamanin da, wanda yanzu kusan an daina amfani da shi saboda zuwan tekanolojin zamani nayin kayayyakin zuba abinci kala-kala, amma har yanzu idan kaje wasu ƙauyuka musamman a arewacin Najeriya suna amfani da shi Akushi. Shi dai Akushi masu yin sana'ar sassaƙa sune suke sassaƙa shi daga bishiya.

A takaice Akushi sassaƙaƙƙen mazubin abinci ne wanda ake amfani da shi kafin zuwan kwanon zuba abinci a ƙasar Hausa wani lokacin ma har da cokali ake sassaƙawa.[1][2]

  1. "Akushi". rumbunilimi.com.ng. Archived from the original on 15 June 2021. Retrieved 15 September 2021.
  2. Musa, Aisha (17 March 2017). "Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya". legit.hausa.ng. Retrieved 15 September 2021.