Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook
Jump to content

Cécile Manorohanta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Cécile Manorohanta
Prime Minister of Madagascar (en) Fassara

18 Disamba 2009 - 20 Disamba 2009
Rayuwa
Haihuwa 20 century
ƙasa Madagaskar
Ƴan uwa
Abokiyar zama Jean Adolphe Dominique (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Cécile Manorohanta (Cécile Marie Ange Manorohanta) 'yar siyasa ce ‘yar Madagascar wacce ke aiki a gwamnatin Madagascar a matsayin mataimakiyar Firayim Minista na cikin gida tun daga shekara ta 2009. A baya ta zamo Ministan Tsaro daga 2007 zuwa 2009.

An nada Manorohanta a mukamin ministan tsaro a ranar 27 ga Oktoba 2007 a gwamnatin Firayim Minista Charles Rabemananjara . Ita ce mace ta farko da ta zamo ministan tsaro a kasar ta.

A ranar 9 ga watan Fabrairun shekara ta 2009, Manorohanta ta sanar cewa zatayi murabus, tana mai cewa "bayan duk abin da ya faru, na yanke shawara a yanzu ba zan kasance cikin wannan gwamnati ba, " [1] tana nufin harbi na ranar 7 ga watan Fabira, a lokacin zanga-zangar Madagascar ta 2009, inda 'yan sanda suka harbe akalla masu zanga-zanga mutum 50. [2] An nada shugaban ma'aikatan soja Mamy Ranaivoniarivo don maye gurbin Manorohanta a wannan rana.[3]

A karkashin shugaban rikon kwarya Andry Rajoelina, an sake nada Manorohanta a mukamin siyasa matsayin Mataimakiyar Firayim Ministan Cikin Gida a ranar 8 ga Satumba 2009. [4][5]

A ranar 18 ga watan Disamban shekara ta 2009, Rajoelina ya sauke Firayim Minista Eugene Mangalaza, wanda bangarorin adawa suka amince da nadin a matsayin wani bangare na yarjejeniyar raba iko, kuma ya bayyana cewa zai nada Manorohanta a madadinsa. Duk da hakan, a ranar 20 ga Disamba 2009 Rajoelina a maimakon haka ya nada Albert Camille Vital a matsayin Firayim Minista.

Tun daga shekarar 2013 ta kasance shugabar Jami'ar Antsiranana .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Madagascar defense minister resigns
  2. "Madagascar protesters shot dead". Al Jazeera. 2009-02-08. Retrieved 2009-02-08.
  3. "Defence minister quits over Madagascar bloodbath", AFP, 9 February 2009.
  4. "SADC 'rejects, condemns' new Madagascar govt", AFP, 8 September 2009.
  5. "Monja Roindefo; Un gouvernement de 31 membres", Madagascar Tribune, 9 September 2009 (in French).
Political offices
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}

Samfuri:MadagascarPMs