Yadda al’umma suka tashi tsaye don yaƙi da matsalar tsaro a Afirka ta Kudu

Abel Rapelego
Bayanan hoto, Abel Rapelego ya tawagarsa ta 'yan sa kai na taimaka wa wajen kare jama'a
  • Marubuci, Ayanda Charlie & Tamasin Ford
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye, Johannesburg & London

Matsalar rashin tsaro da ayyukan 'yan daba na cikin abubuwan da ke ci wa al'ummar Afirka ta Kudu tuwo a ƙwarya, a yayin da suke shirin fita rumfunan zaɓe domin zaɓen sabon shugaban a ƙarshen watan da muke ciki.

'Yan siyasar ƙasar sun sha yi wa al'ummar alƙawuran magance matsalolin da zarar jam'iyyunsu sun samu nasara a zaɓen da ke tafe.

A yayin da alƙaluman kisan kai suka kai matakin da ba su taɓa kai wa ba cikin shekara 20, sashen bin ƙwaƙwaf na BBC ya samu shiga ɗaya daga cikin unguwannin da ke fama da matsalar.

Bayan da ƙarar busa usur ta cika unguwar, mutane sanye da riguna masu launin ruwan lemo da ruwan ɗorawa na ta guduwa.

“Wayyo Allah,” Wani ɗan sanda ne ya yi ƙara a lokacin da ya faɗi ƙasa, bayan da aka harbe shi.

Ranar wata Juma'a a daddare a unguwar Diepsloot, wani ƙaramin gari a wajen birnin Johannesburg, cibiyar kasuwar ƙasar Afirka ta Kudu.

“Wannan abu ne da ke faruwa koyaushe,” in ji Abel Rapelego, shugaban tawagar 'yan sa kan da ke gudanar da sintiri a kan titunan unguwar.

Jiniyar motar 'yan sanda ta tarwatsa cincirindun mutanen da suka taru a wata daba.

“Ku 'yan sa kai ku koma gefe!” mista Rapelego ya gaya wa tawagarsa da ƙarfi. “Mu bari jami'an 'yan sanda su yi aikinsu.”

An garzaya da jami'in ɗan sandan da aka harbe mai shekara 38, mai suna Tom Mashele zuwa sibiti, amma sai dai ya mutu bayan makonni.

Babu wanda aka kama da laifin kisan ɗan sandan - wanda ya aka kashe a lokacin da yake hutu.

The volunteer patrollers at work
Bayanan hoto, 'Yan sa kan kan tsayar da duk mutumin da ba su yarda da shi ba domin yi masa tambayoyi

Afirka ta Kudu na daya daga cikin ƙasashen da aka fi samun laifukan kisan kai a duniya, kamar yadda alƙaluman ofishijn kula da laifuka da miyagun ƙwayoyi na Majalisar Dinkin Duniya suka nuna.

A shekarar da ta gabata an samu lamuran kisan kai 27,000 a ƙasar, wanda hakan ke nufin a cikin mutum 100,000 da suka mutu 45 kashe su aka yi, fiye da na Amurka inda ake samu shida cikin 100,000 .

A kan haka ne, Mista Rapelego ya ce hanya ɗaya tilo da suke bi domin kare rayukan iyalansu, shi ne 'yan sa kai riƙa sintiri a unguwanninsu, koda kuwa hakan zai sa su sanya rayukansu cikin hatsari, saboda a cewarsa ''ɓata gari ne ke iko da unguwar Diepsloot''.

Tawagar 'yan kai kai na aiki ne kafaɗa da kafaɗa da 'yan sandan birnin Johannesburg.

Aikin haɗin gwiwa ne wanda ba hukumace ta tanadi hakan be.

Babu wanda ke biyan 'yan sa kan kuma ba sa riƙe bindiga, amma suna da tufafin gargajiya da suke sanyawa ta yadda ake iya gane su cikin jama'a.

“Mukan riƙa bincikar mutanen da ba mu yarda da su ba, kuma duk mutumin da ya i ba mu haɗin kai, muna ɗaukar mataki a kansa,'' in ji mista Rapelego.

Ƙungiyar sa kan ba ta da hurumin kafa shingen bincike domin gudanar da ayyukanta, amma takan shiga unguwanni domin bincikar duk mutanen da ba ta amince da su ba.

A yayin da suke wucewa ta ƙofar wani shago, mai shagon ya faɗa musu cewa an yi masa fashi, nan take 'yan sa kan suka ƙaddamar da bincike in da a ka kama wani mutum da suka gani a guje, suka kuma chaje shi, domin ganin wayoyi dakuɗaɗen da ake sace wa mai shagon.

Alƙaluman aikata miyagun laifuka a Afirka ta Kudu sun nuna cewa waɗanda ake kashewan matasa ne baƙaƙen fata, lamarin da ake ganin 'yan sa kan na jefa rayukansu cikin hatsari.

Shekara biyu da suka gabata aka harbe Alpha Rikhotso, mai shekara 21, a lokacinj da yake kan aikin sintirin, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.

“Ina ƙoƙarin sabawa da yanayin, amma abin akwai takaici da ciwo ,'' in ji mahaifinsa, David Rikhotso.

“An kashe shi a lokacin da yake ƙoƙarin kare ransa da na iyalansa da na kowa aunguwar nan, yana faɗa ne a kan aikata miyagun laifuka.”

Someone showing a picture on a phone
Bayanan hoto, David Rikhotso ke nuna hoton ɗansa, Alpha, wanda aka harbe shekara biyu da suka gabata

Ɗan nasa ne mutum na farko da ke wurin a lokacin da 'yan sa kai suka hura usur dopmin ankarar da jama'a game da ayyukan ɓata garin a wurin.

Yaron ya yi yunƙurin kama ɗaya daga cikin masu aikata laifin, inda suka harbe shi.

Nan take ya rasu, saɓanin jami'ain ɗan sandan, kuma shi ma babu wanda aka kama da laifin kisan.

“A kowave rana aka yi wa mutane fashi.Mutane na mutuwa a kullum. A kowace rabna addu'a nake yi Allah ya ba su ('Yan sa kan) kariya. Babu dokar da ke aiki a wannan wuri,” kamar yadda mista Rikhotso ya shaida wa sahen binciken ƙwaƙwaf na BBC.

ayyukan ɓata garin na janyo wa gwamnati mummunar asara ta fuskar tattalin arziki.

Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa asarar da ayyukan ɓata garin ke janyo wa Afirka ta Kudu ya kai dala biliyan 40 a kowace shekara, watokusan kashi 10 na kuɗin shighar ƙasar.

Kuma matsalar ta shafi kusan duka al'umma da ƙabilun ƙasar.

Wasu 'yan sa kan sun kafa tawagarsu domin yaƙar irin waɗannan ayyuka a garin Brits dake lardin Arewa maso yamma, mai jisan kilomita 60 daga garin Diepsloot

A garin manoma ne suka haɗa tawagar sa kan da suka kira Afriforum, Sun ce suna wakilita fararen fatar Afirka, kuma suna da mambobi 300,000 a ƙasar.

Suna amfani da motoci da babaura da ma jirage marasa matuƙa domin yin bincike a gonaki da gine-ginen da ba a kammala ba a tsawon dare domin zaƙulo ɓata0garin.

Sun ce suna duba kayyakin da aka sace, tare da tsayar da duk wanda ya yi dare domin bincikarsa.

Da yawa daga cikinsu na ɗauke da makamai, kamar Dewald van Wyngaardt.

“Bai kamata ka je da wuƙa wurin da ake yaƙi da bindiga ba. Dolene nakare iyalaina, wannan shi ne, Indai zan je wurin wanda zai yaƙe ni, to dole ni ma na je da shirina,'' in ji shi.

Volunteers looking at a camera
Bayanan hoto, 'Yan sa kan Afriforum na lokacin da suke bakin aiki.

Hare-haren da ake kai wa manoma fararen fata a Afirka ta Kudu na ci gaba da ɗaukar hankalin duniya.

A shekarar 2018, shugaban Amurka na wancan lokacin, Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na X, wanda a lokacin aka fi sani da Twitter, yana mai cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na ƙwace gonakin fararen fata, wanda ba gaskiya ba ne. Ya kuma ce ana ''kashe manoma masu yawa''

A watan Yulin shekarar da ta gabata, shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, wanda haifaffen birnin Pretoria ne ya wallafa shafinsa na X ɗin dangane da jam'iyyar adawa yana mai cewa ''Suna ƙoƙarin ƙarfafa yi wa fararen fata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu''.

To sai babu wata hujja da ke nuna cewa fararen fata sun fi kowa shiga cikin hatsari a ƙasar.

Alƙaluman hukuma sun nuna cewa fararen fata a Afirka ta kudu da kaɗan suka haura kashi 7 cikin 100 na al'ummar ƙasar, to amma su ne ƙasa da kashi biyu na mutanen da ake kashewa, haka kuma fargabar da manomanƙasar ke da ita na ƙaruwa.

“Muna rayuwa ne tamkar a cikin keji wanda kuma hakan bai dace ba, idan akwai abu guda da ya kamata a kawar a ƙasar nan to dabanci ne,'' in ji mista De Klerk.

'Yan sanda sun ce wannan abu ne da ba za a lamunta ba, kuma a cikin wata sanarwa da suka aike wa BBC, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar ya ce 'yan sanda sun shirya kawar da ayyukan ɓata garin.

"Ciki har da ɗaukar 'yan sanda masu yawa da suka kai 30,000 cikin shekara uku, ''sannan kuma an ninka kasafin kuɗin 'yan sanda a cikin shekara uku.