Yadda ƴanmata ke ƙirƙirar manhajoji a Arewacin Najeriya

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Yadda ƴanmata ke ƙirƙirar manhajoji a Arewacin Najeriya

Ana iya ƙarfafa gwiwar mata a arewacin Najeriya, har su cimma burinsu na rayuwa, ta hanyar jan hankulansu cikin harkokin fasahar sadarwar zamani.

Wata matashiya da ta kafa Cibiyar Startup Kano, Aisha Tofa ce ta nunar da haka lokacin da take jawabi game da ayyukan cibiyarta da ke ƙyanƙyashe tunanin kafa sana'o'i.

Ta ce ta kafa cibiyar ce lokacin da ta kammala jami'a amma samun yi, ya zame mata ƙalubale.

Ta dai shawarci matasa a kan su zage wajen neman ilmi musamman na fasahar sadarwar zamani don kuwa in ji matashiyar, nan hankalin duniya ya karkata.