Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook
Isa ga babban shafi

Amurka ta caccaki Isra'ila amma za ta ci gaba da ba ta makamai

Yayin da rahotanni ke cewa adadin fararen hular da suka mutu a Gaza ya haura dubu 35, Amurka ta fitar da wani rahoto da ke chachakar Isra’ila kan ci gaba da yunkurin farwa Rafah, sai dai duk da haka ta ce ba zata dakatar da bata tallafin makamai ba.

Sugaban Amurka, Joe Biden.
Sugaban Amurka, Joe Biden. REUTERS - Elizabeth Frantz
Talla

Rahoton na Amurka wanda aka jima ana jira ya ce akwai yiwuwar Isra’ila ta take dokokin yaki na duniya ta hanyar amfani da makamai, sai dai kuma ba ta sami cikakkun dalilan da za su hana ta ci gaba da bai wa kasar tallafin makamai ba.

Rahoton ya ci gaba da cewa alamu da yawa sun nuna cewa Isra’ila ta yi amfani da makaman da Amurka ta ba ta wanda darajar su ta kai dala biliyan 3 wajen take hakkin dan adam da kuma cin zarafin fararen hula.

Rahoton ya zo ne bayan shafe kwanaki ana tafka muhawara a sashen binciken sirri na Amurka kan ko za’a iya kama Isra’ila da laifin yaki ko kuma akasin haka.

Haka kuma ƙarin bayani da hukumar binciken sirrin Amurka ta fitar ne kwanaki biyu kacal bayan da shugaban kasar Joe Biden ya yi barazanar dakatar da wasu bama-bamai da makaman atilari matukar kasar ta fara kai hare-hare Rafah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.