Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Da Tarayyar Turai sun Dauki Matakan Kawo Karshen Sana’ar Safarar Bakin Haure


Shugaba Bazoum Muhamed na kasar Nijar
Shugaba Bazoum Muhamed na kasar Nijar

Tarayyar Turai ta ce yarjejeniyar yaki da safarar bakin haure da ta kulla da Nijar ka iya taimakawa matuka wajen kakkabe 'yan baranda masu mummunar tabi’ar nan ta safarar bakin haure zuwa nahiyar Turai

Jamhuriyar Nijar da Tarayya Turai sun tsaurara matakan yaki da masu sana’ar safarar bakin haure. kasashen biyu dai sun cimma yarjejeniyar ce ayayin ziyarar da Jakadiyar Tarayyar Turai ta kawo a Nijar inda suka kudiri aniyar kawo karshen safarar bakin haure.

Sai dai matasan da suka bar wannan aikin sun bayyana cewa ana tafiyar hawainiya wajen cika alkawuran da akayi musu na samar musu da aikin yi na halal.

Bayan shafe tsawan shekaru tana zama hanyar da bakin haure ke bi daga yammaci Africa, Jamhuriyar Nijar ta hada kai da kungiyar Tarayyar Turai don magance wannan matsalar.

NIGER: Wani taron kasa da kasa kan bakin haure a Nijar
NIGER: Wani taron kasa da kasa kan bakin haure a Nijar

Tarayyar dai Turai tace yarjejeniyar yaki da safarar bakin haure da ta kulla da Nijar ka iya taimakawa matuka wajen kakkabe 'yan baranda masu mummunar tabi’ar nan ta safarar bakin haure zuwa nahiyar Turai.

Ahmdu Umaru, shugaban kungiyar tsofaffin masu safarar bakin haure, ya bayyana yadda suke kallon sabuwar yarjejeniyar.

Alkawura da dama ne aka yi wa matasa na samar musu da ayyukan da zasu maye gurbin sana’ar safarar bakin haure. Saidai babu wani labari mai gamsarwa da ya shafi alkawuran inji Mohamed Aghali, shugaban wata kungiyar matasa.

A Nijar matasan da suka yi watsi da safarar bakin haure su 6500 ne za a taimakawa da aikin yi. Saidai shekaru bakwai bayan daukar alkawarin mutun 900 ne kawai suka ci gajiyar wannan shirin. Saidai kungiyoyin farar hula na ganin wannan batun hana safarar bakin haure na da wuyar aikatawa, inji Malan Abdulkarim dan kungiyar farar fula.

Tun da jimawa Nijar ke zama wata hanya tilo daya ta kwararar bakin haure daga kasashen Afurka ta Yamma da dama wadanda ke shiga Libiya da zummar zuwa Turai ta barauniyar hanya.

Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG