Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Na Sha'awar Wakokin Wasu 'Yan Najeriya Hudu


Obama na sha'awar wakokin 'yan Najeriya
Obama na sha'awar wakokin 'yan Najeriya

A ci gaba da taka rawar gani da 'yan Najeriya ke yi a fagage da dama na rayuwar dan adam a duniya, daga cikin 'yan Afurka biyar da tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama, ya zaba a bazarar Summer ta wannan shekarar, hudu 'yan Najeriya ne.

Tsohon Shugaban na Amurka, Barack Obama, ya sa wakokinsu cikin jerin sunayen mawakan da ya ke saurare a lokacin bazarar Summer ta 2022, a cewar mujallar NNPC MONTHLY wacce ake bugawa wata wata.

Obama ya wallafa jerin sunayen gwanayen nasa ne a shafin kafar sada zumunta ta Instagram na @Barack Obama jiya Talata, 26 ga watan Yuli.

“Kowace shekara, na kan yi farin cikin bayyana mawakan da na zaba don saurare a lokacin summer saboda na samu labaran wasu mawaka da dama daga irin ra’ayoyin da ku ke bayarwa a matsayin martani – wannan wani misali ne na irin yadda sha’awar wakoki ke iya hada kanmu duka. Ga irin wakokin da na ke saurare a wannan bazarar Summer. Wadanne wakoki za ku kara?” a cewar Obama.

Kowace shekara, Obama yakan rubuta sunayen wakokin da ya fi sha’awa daga daban daban na duniya.

Ita kuma jaridar Premium Times ta bayyana sunayen makawan na Najeriya da Obama ya zaba da: Tems, Burma Boy, Buju, da Pheelz. Premium Times ta ce bayan ‘yan Najeriyan, dan wata kasar Afurka daya ne kawai, wato Sampa the Great, wani dan Zambia mazunin kasar Australia wanda kuma ke rubuta wakoki da wakar rab (mai kamar gambara).

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG