Me ke janyo makanta rana tsaka?

Wani mutum mai lalurar makamanta

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Aisha Babangida
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
  • Aiko rahoto daga Abuja

Samun makanta rana tsaka ba zato ba tsammani na iya shafar kowane fanni na rayuwar mutum - wato sabuwar rayuwa za ta fara wadda take daban da wadda mutum ya saba yi a lokacin da yake gani.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce aƙalla mutane biliyan 2.2 suna da matsalar ganin kusa ko nesa a duniya, wadda akan iya kare biliyan ɗaya na waɗannan daga makanta rana tsaka.

Dakta Mutspha Muhammad Hafiz likitan ido ne a asibitin ido na tarayya da ke Kaduna kuma ya bayyana abin da ake nufi da makanta ta rana tsaka.

"Irin makantar da mutum haka kawai zai daina gani, kwastam ya fara ganin duhu, yawanci wata cuta ce da ke tattare da mutum ko kuma wani tsautsayi ke haddasa ta," in ji shi.

Abubuwan da ke janyo makanta

...

Asalin hoton, SMIRART/GETTY IMAGES

Akwai dalilai da dama da ke janyo samun makanta ta lokaci guda, kamar yadda likitan ya yi bayani.

Fashewar hanyoyin jini: Baki ɗayan hanyoyin jini - da ke kaiwa da kuma dawo da jini ga ido - duk wadda ta fashe cikinsu za ta iya janyo makanta.

Hakan nan kuma, ciwon kai me tsanani yana iya haddasa wa mutum makanta, wannan amma yakan zo ne lokaci ɗaya kuma ya daidaita bayan wasu lokuta.

Cutuka: Ciwon hawan jini da ciwon suga masu tsanani, da sikila, da ciwon daji, suna iya toshe hanyoyin da ke kai jini zuwa ido, wanda zai iya kawo makanta a hankali ga mutum idan suka taɓa wasu sassa na idanu masu muhimmanci da abin da ya shafi gani.

Ɗayewar Zinariyar Idanu: Akwai zinariya ta idanu wadda take bayan ido da ke sarrafa haske kum ta tura wa ƙwaƙwalwa har da zai saka mutum ya iya tantance launi.

Wannan zinariyar tana iya ɗayewa daga mazauninta wanda shi ma ke janyo makanta.

Iska mai ƙarfi da ke tafe da ɓuraguzai: Rauni daga duka, ko iska mai karfi da ke ɗauke da abubuwa kamar ƙarafuna, ko ƙusa, ko allurai, ko ƙasa, ko gurɓataccen muhali, ko bugewa, ko jifa, ko amfani da sanda a kan ido, su ma ka iya janyo makanta idan har ya taɓa sassan ido da bai makata ba.

Amfani da abubuwa barkatai a ido: Dakta Mustapha ya ƙara da cewa yawan amfani da magunguna barakatai, ko amfani da wasu abubuwa kamar fitsari ko kashin shanu, ko ganyeyyaki da ake shafa wa a cikin ido, ko kuma sauran abubuwan da ake haɗawa cikin kwalli da sunan maganin ciwon ido - ba tare da an tuntuɓi ƙwararen likita ba - za su iya janyo mutum ya samu matsalar gani.

Wasa da abubuwa masu haɗari: Irin abubuwan da yara ke amfani da su wajen wasa kamar su danƙon harbi, duk za su iya kawo wa mutum matsala a ido idan har sun taɓa sashen da bai kamata ba.

Ta yaya za a samu kariya daga makanta ta lokaci guda?

Likitan ya ce zuwa asibiti akai-akai don duba lafiyar idon mutum na ɗaya daga cikin babban matakin kariya da zai iya ɗauka.

"Yana da muhimmanci haka kawai mutum ya je a duba lafiyar idonsa, musamman waɗanda suka yi shekara 40 da abin da ya yi sama, saboda galibi ciwon ido ya fi bayyana ga waɗannan mutane." In ji Dakta Mustapha.

Likitan ya kuma ce waɗanda ke da ciwon ido a cikin zuriyarsu, shi ma yana da kyau ya je a dinga duba masa lafiyar idonsa ko da ba su da alama ta wata lalura.

Ya kuma ce mutane su dage da amfani da duk abin da ya shafi kariya ta ido daga rauni musamman ga waɗanda aikinsu ya shafi tsautsayi ga ido, kamar masu walda da masu acaɓa, da iska ke dukan fuskarsu kodayaushe, da masu sana'ar kafinta, da kanikawa, da ma waɗanda ke amfani da kamfutoci.

Dangane da masu fama da ciwon hawan jini da na suga, likitan ya ce: "Bayan kula da hawan jinin da ciwon suga da ake yi, ya kamata su dinga samun awon ido ko duba lafiyar idonsu lokaci-lokaci saboda a ɗauki matakin da ya kamata idan an gano wata matsala dangane da idon.

"Muna kuma shawartar duk wanda ya ji alamun ciwon ido ko ya samu rauni ya kiyaye ɗaukar mataki da kansa, ya dage da zuwa asibiti."

Akwai maganin makanta rana tsaka?

Dakta Mustapha ya ce maganin makanta rana tsaka ya dangata da abin da ya haddasa ɗaukewar ganin nan take.

Ya ce kowane dalili na samun ciwon makantar na da hanyar magance shi, inda ya ƙara da cewa ya dangata har wa yau ga saurin da mutum ya yi zuwa asibiti "saboda nasarar da ake samu wajen magani idan mutum ya je asibiti da wuri ya fi ga wanda ya je a makare".

"Idan an je asibiti da wuri, kamar irin toshewar hanyoyin jinin da ke kai wa ido, akwai abin da ake yi nan take domin a ga hanyoyin jinin sun buɗe kuma jini ya ci gaba da kwaranya zuwa sassa daban-daban na ido ba tare da wata matsala ba." In ji Dakta Mustapha.