Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu A Harin Rasha Sun Kai 115


APTOPIX Russia Shooting
APTOPIX Russia Shooting

A ranar Asabar Rasha ta ce ta kama mutane 11 - ciki har da ‘yan bindiga hudu, kan harin da aka kai a wani zauren raye-raye na Moscow da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 115.

Har yanzu shugaban kasar Rasha Vladimir Putin bai ce uffan ba kan harin, kuma Moscow ba ta yi magana kan ikirarin kungiyar IS ba, kamar yadda wasu ‘yan majalisar dokokin kasar suka nuna yiwuwar alaka da Ukraine.

Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun bude wuta a dakin taro na Crocus City Hall da ke yankin Krasnogorsk na arewacin birnin Moscow a yammacin ranar Juma’a, gabanin wani wasan wake-wake da kungiyar zamanin Soviet ta Piknik za ta yi, a wani mummunan harin da ba'a ga irinsa ba akalla shekaru goma a Rasha.

Hukumar tsaro ta FSB ta Rasha ta ce, wasu daga cikin wadanda suka aikata laifin sun tsere zuwa kan iyakar Rasha da Ukraine, inda ta kara da cewa maharan suna da alaka da wasu a kasar.

Bata bayar da karin bayani ba.

Wasu ‘yan majalisar dokokin Rasha ma sun nuna yatsa ga Ukraine, ba tare da bayar da wata shaida ba.

“Babbar wadda za ta kasance da hannu na iya zama Ukraine da abokanta...ba za mu iya kawar da tunanin hakan ba,” in ji babban dan majalisar dokokin Rasha Andrey Kartapolov.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG