Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kuma: Wasu Mata Na Zargin Diddy Da Yi Musu Fyade


2022 BET Awards - Arrivals
2022 BET Awards - Arrivals

Daya daga cikinsu ta ce Diddy ya taba zuba mata kwayoyi a abinci ya kuma yi mata fyade har da dauka a bidiyo ba tare da saninta ba

Wasu mata biyu sun sake fitowa suna zargin fitaccen mawakin Amurka Sean Combs wanda aka fi sani da Diddy da yi musu fyade a shekarun 1990.

Bayyanar wadannan mata da wannan zargi na zuwa ne kwanaki bayan da Diddy da Cassie suka sulhunta kan zargin da ta yi masa na cin zarafinta ta hanyar fyade.

Cassie wacce ita ma mawakiya ce kuma asalin sunanta Cassandra Ventura ta shigar da Diddy kara a gaban kotu inda ta zarge shi da yi mata fyade.

Kwanaki bayan shigar da karar Cassie ta janye suka sasanta a wajen kotu da Diddy.

Sai dai a ranar Juma’a wasu mata biyu sun sake bayyana wadanda suke zargin Diddy da yi musu fyade, inda suka shigar da kara a kotu.

Daya daga cikinsu ta ce Diddy ya taba zuba mata kwaya a abinci ya kuma yi mata fyade har da dauka a bidiyo ba tare da saninta ba.

Matar ta biyu, wacce ba a fadi sunanta ba, ta ce Diddy da wani abokinsa sun yi mata fyaden taron dangi ita da wata kawarta bayan da aka kammala wani fati.

Sai dai Kakakin Diddy, ya musanta dukkan zarge-zargen.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG