Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Blinken Ya Ce Amurka Za Ta Ba Da Karin Dala Miliyan 133 Don Tallafawa Kasar Haiti


Blinken yayin ziyararsa zuwa Haiti
Blinken yayin ziyararsa zuwa Haiti

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a  Litinin din nan ya yi alkawarin karin dala miliyan 133 don tallafawa kasar Haiti, yana mai cewa, rikicin da ke kara kamari ya nuna  butar gaggawa na  tura dakaru na kasa da kasa.

Da yake jawabi a wani taron gaggawa na yankin Caribbean a Jamaica, Blinken ya ce Amurka za ta sake ba da karin dala miliyan 100 ga Ofishin Taimakon Tsaro na Kasa da Kasa, tare da taimakon dala miliyan 33 nan take na ayyukan jinkai, wanda ya kawo jimillar alkawurran da Amurka ta yi wa Haiti na rikicin tsawon shekaru da dama zuwa dala miliyan 333.

Haiti
Haiti

Haiti dai ta sha fama da talauci shekaru da dama, da bala'o'i da kuma rashin zaman lafiya na siyasa amma al'amura sun kara ta'azzara tun bayan kisan shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021. Gungun masu rike da makamai da ke rike da galibin ikon kasar da galibin babban birnin kasar sun yi ta aika-aika tun makon da ya gabata.

Rikicin da ke kara ta'azzara "yana haifar da yanayi mara kyau ga al'ummar Haiti, kuma duk mun san cewa ana bukatar daukar matakin gaggawa duka kan hanyoyin siyasa da tsaro," in ji Blinken.

"Mutanen Haiti ne kawai za su iya tantance makomarsu - ba wasu ba," in ji Blinken.

Blinken
Blinken

Amma ya ce Amurka da kawayenta "za su iya taimakawa wajen maido da tushen tsaro" da kuma magance "mummunar wahalhalul da kasar Haiti ke ciki."

Shima Firayim Ministar Kanada, Justin Trudeau, ya tallafa da sama da dalar Amurka miliyan 91 ga Haiti.

Sauran kasashen da suka ba da sanarwar bayar da gudummuwar kudi ko kayan aiki sun hada da Benin, Faransa, Jamus, Jamaica da Spain, a cewar jami’an Amurka.

Shugaba Joe Biden ya yi watsi da batun tura dakaru zuwa Haiti, wadda Amurka ta mamaye kusan shekaru 20 da suka gabata, inda ta shiga tsakani tun daga lokacin.

Biden ya janye sojoji daga Afghanistan a shekarar 2021 kuma ya sha alwashin takaita hadurran da sojojin Amurka ke fuskanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG