Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gadar Baltimore Ta Dare Bayan Jirgin Ruwa Ya Ci karo Da Ita


Gadar Baltimore a Jihar Maryland - Key Bridge Baltimore
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:31 0:00

Gadar Baltimore a Jihar Maryland - Key Bridge Baltimore

Wani jirgin ruwan mai dakon kwantena ya kutsa cikin wata babbar gada da ke Baltimore a jihar Maryland da sanyin safiyar Talata, lamarin da ya yi sanadin karyewarta a wasu wurare tare da nutsewa cikin kogi.

WASHINGTON, D. C. - Motoci da dama sun fada cikin ruwan mai tsananin sanyi, kuma da farko masu aikin ceto sun fara neman akalla mutane bakwai ne.

MARYLAND-BRIDGE
MARYLAND-BRIDGE

An samu ciro mutane biyu daga cikin ruwan da ke karkashin gadar Francis Scott Key Bridge, inda daya na cikin mawuyacin hali, a cewar Shugaban hukumar yaki da gobara na Baltimore James Wallace.

Da alama jirgin mai dakon kaya ya daki kan daya daga cikin matsayar gadar ne a tsakiyar dare lokacin da ake sa ran babu masu zirga-zirgar da yawa, a cewar wani faifan bidiyo da aka wallafa akan X (Twitter). Jirgin ya kama da wuta, kuma hayaki mai kauri na tashi daga cikinta.

Francis Scott Key Bridge Baltimore, Maryland, March 26, 2024.
Francis Scott Key Bridge Baltimore, Maryland, March 26, 2024.

Kamfanin Sonar ya yi nuni da cewa, motoci sun fada cikin ruwan, inda sanyi ya kai kimanin digiri 47 na Fahrenheit kwatankwacin digiri 8 na Celcius da sanyin safiyar Talata, a cewar wani mai tattara bayanai na hukumar kula da harkokin teku da iska ta kasa.

Tun da farko, Kevin Cartwright, darektan sadarwa na hukumar yaki da gobara na Baltimore, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa, a lokacin da lamarin ya afku akwai wasu motoci da dama a kan gadar, ciki har da wata mai girman tarakta.

Maryland Bridge
Maryland Bridge

Gwamnan jihar Maryland Wes Moore ya ayyana dokar ta-baci kuma ya ce yana bakin kokarinsa wajen neman taimako daga gwamnatin tarayya. Hukumar FBI ma tana wurin.

An dai bude gadar mai layi hudu a shekarar 1977, shekaru biyar bayan a gina ta kuma tana da tazarar mil 1.6 kwatankwacin kilomita 2.6.

US-Maryland Bridge
US-Maryland Bridge

Ya ketare kogin Patapsco, inda marubucin wakokin kasar Amurka Francis Scott Key ya rubuta "Star Spangled Banner" a shekara ta 1814 bayan ya shaida yadda Birtaniyya ta sha kaye a yakin Baltimore da kuma harin bam na Birtaniya na Fort McHenry.

Gadar na da tsayin 185 (mita 56) a tsaye. Ta na kuma daukar motoci miliyan 11.3 a duk shekara, in ji Hukumar Kula da Sufuri ta Maryland, akan babbar hanyar I-695 da ke zagaye da Baltimore, wacce aka fi sani da Baltimore Beltway.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG