Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Gargadi Kasashen Turai Hudu Kan Amincewa Da Kafa Kasar Falasdinu


Netanyahu
Netanyahu

Isra'ila ta fadawa wasu kasashen Turai hudu a yau Litinin cewa shirinsu na yin aiki don amincewa da kafa kasar Falasdinu ya zama "daukaka wa ta'addanci" wanda zai rage damar yin shawarwari na kawo karshen rikicin da ke tsakanin makwabtan.

WASHINGTON, D. C. - Kasar Spain ta fada a ranar Juma'a cewa, don samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, ta amince da kasashen Ireland, Malta da Slovenia, da su dauki matakin farko na amincewa da kafa kasa da Falasdinawan suka ayyana a yammacin gabar kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye da kuma a zirin Gaza.

Gaza ta dade tana karkashin ikon kungiyar Hamas mai kishin Islama, wadda ta ki amincewa da zaman lafiya da Isra'ila, ta kuma kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya haifar da mummunan yakin da ya haddasa tashin hankali a yammacin gabar kogin Jordan, inda Isra'ila ke da matsugunan Yahudawa masu yawa.

"Amincewa da kasar Falasdinu bayan kisan kiyashin na ranar 7 ga watan Oktoba yana aike ne da sako ga kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin ta'addanci na Palasdinawa cewa za a mayar da martani ga harin ta'addanci na kisan gilla kan 'yan Isra'ila tare da nuna alamun siyasa ga Falasdinawa," in ji Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Israel Katz a kan shafinsa na X wadda a da aka fi sani da Twitter.

"Maganin rikicin ba zai yiwu ba ne kawai ta hanyar yin shawarwari kai tsaye tsakanin bangarorin. Duk wani aiki na amincewa da kasar Falasdinu kawai zai kai ga cimma matsaya da kuma kara rashin zaman lafiya a yankin."

Bai fayyace ko wane irin kuduri yake da shi ba. Isra'ila, wadda kawancen gwamnatinta ya hada da masu ra'ayin mazan jiya, ta dade tana kawar da maganar kafa kasar Falasdinu.

Hakan dai ya sa ta yi takun-saka da manyan kasashen yammacin duniya wadanda ke goyon bayan burinta na kayar da Hamas amma suna son tsarin diflomasiyya bayan yakin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG