Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paul Alexander, Majinyacin Da Ke Numfashi Da Huhun Karfe Ya Mutu


Paul Alexander
Paul Alexander

Paul Alexander ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 78, a cewar wata sanarwa da dan'uwansa, Philip Alexander, ya fitar ta kafar sada zumunta.

Paul Alexander, wanda ya mutu yana da shekaru 78 a duniya ya kamu da cutar shan inna yana da shekaru 6, ya kuma rayu na tsawon shekaru 70 yana lumfashi ta wajen amfani da injin numfashi. Duk da haka, ya sami damar samun digiri na shari’a, ya kuma rubuta littafi.

Bayan da cutar shan inna ta shanye shi yana a shekara 6, lamarin ya tilastawa Paul Alexander dogara ga amfani da huhun karfe.

Paul Alexander
Paul Alexander

Rayuwa a cikin huhun karfe sakamakon kamuwa da cutar shan inna bai hana Alexander zuwa jami'a ba, ya sami digiri na shari'a da kuma aikin lauya fiye da shekaru 30 da suka shige. Sa’ad da yake yaro, ya koya wa kansa numfashi na tsawon mintuna da sa’o’i a lokaci guda, duk da haka ya zama dole ya yi amfani da injin a kowace rana ta rayuwarsa.

Ya kasance daya daga cikin mutane kadan da su ka rage a Amurka da ke zaune a cikin huhun karfe. Kuma a cikin makonnin karshe na rayuwarsa, ya nuna wa mabiyansa na TikTok yadda ya ke rayuwarsa da taimakon injin.

Ba a bayyana dalilin mutuwarsa a hukumance ba. Amma Alexander ya dan jima yana asibiti don ya kamu da cutar Covid-19 a watan Fabrairu, a cewar shafinsa na TikTok. Bayan ya koma gida, Alexander ya yi fama da rashin cin abinci da shan ruwa yayin da yake murmurewa daga cutar, wacce ke afkawa huhu kuma tana iya zama hadari musamman ga mutanen da suka tsufa kuma suna da matsalar numfashi.

Alexander ya kamu da cutar shan inna a shekara ta 1952, a cewar littafinsa, “Three Minutes for a Dog: My Life in an Iron Lung.” wanda ya rubuta ta hanyar sanya alkalami ko fensir a bakinsa. Nan take likitocin asibitin Parkland da ke Dallas suka sanya shi cikin huhun karfe domin ya samu yin numfashi.

Lokacin da yake cikin injin, Alexander yakan bukaci taimakon wasu don ayyuka na yau da kullun kamar ci da sha.

Alexander ya kaddamar da shafin TikTok dinsa a watan Janairu, kuma, tare da taimakon wasu, ya fara kirkirar bidiyo game da rayuwarsa.

A cikin wani bidiyo, Alexander yayi cikakken bayani game da kalubalen tunani da tunani na rayuwa a cikin huhun karfe.

"Akwai kadaici," in ji shi "Wani lokaci ina cikin matsananciyar damuwa saboda ba zan ma iya taba wani ba, hannayena ba sa motsowa."

Alexander ya fada a cikin bidiyon cewa ya shafe shekaru da dama yana samun sakonnin imel da wasiku daga mutanen da ke fama da damuwa da kadaici, ya kuma basu shawarwari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG