Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahotanni Game Da Bullo Da Shudin Kati A Manyan Gasoshin Kwallon Kafa Ba Gaskiya Bane Kuma Sun Yi Wuri-FIFA


Shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino
Shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino

Hukumar FIFA mai kula da harkokin kwallon kafa ta duniya ta fitar da wata sanarwa da nufin yayyafawa kurar ruwa game da shigo da katin cikin harkar kwallon kafa musamman a manyan gasoshi.

Za’a yi amfani da shudin kati ne domin mayar da dan wasa saniyar ware, kwatankwacin yadda ake hukunta ‘yan wasan kwallon Rugby.

Hakan zai zamo tamkar wani ci gaba ne akan amfani da katin gargadi mai launin rawaya kuma za’a fi amfani da shi ne wajen hukunta ‘yan wasan da suka bijirewa umarnin alkalin wasa.

Jim kadan bayan bayyanar wannan rahoto, aka fara yada jita-jita akan yadda za’a aiwatar da amfani da wannan kati a manyan gasoshi irinsu firimiyar ingila da la-ligar kasar sifaniya. saidai sanarwar da hukumar fifa ta fitar a baya-bayan nan ta fayyace lamarin.

A wani salon sako irin na kafafen sada zumunta, hukumar kwallon kafar duniyar ta bayyana cewar babu kamshin gaskiya a batun bullo da irin wannan kati a manyan gassanin kwallon kafa kuma hakan yayi wuri.

Hukumar ta FIFA ta kara da cewar ba za’a aiwatar da duk wani shiri na bullo da shudin kati ba sai an fara jarraba shi a kananan gasoshi tukunna.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG