Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rema Ya Soke Wasanninsa "Don Ya Kula Da Lafiyarsa"


Rema, hagu, Selena Gomez hagu
Rema, hagu, Selena Gomez hagu

Wannan labari dai bai yi wa masoyansa dadi ba, duba da cewa sun kasa sun tsare don ganin mawakin a wasannin karshen shekara.

Mawakin Afrobeat a Najeriya Rema, ya soke dukkan ragowar wasannin da zai yi a watan Disambar nan da ya kama.

Rema, wanda ya samu karin karbuwa a duniya da wakarsa ta “Calm Down” ya bayyana cewa yana bukatar ya je ya kula da lafiyarsa.

“Ban ji dadi da ba zan yi wasa a wannan wata na Disamba ba, na kwashe shekaru ina ta yawo, na yi watsi da lafiyata, ina bukatar na murmure. 2024 muna nan tafe.” Rema ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Wannan labari dai bai yi wa masoyansa dadi ba, duba da cewa sun kasa sun tsare don ganin mawakin a wasannin karshen shekara.

Tuni dai fitaccen mawaki Davido ya goyi bayan mawakin, inda ya nuna cewa aikinsu, aiki ne da ke cin jiki.

“Aikin babu sauki ga jiki da kwakwalwa. Afirka da duniya na alfahari da kai fiye da yadda ba ka tsammani. Ka je ka huta Sarki @heisrema don ka dawo da karfinka.” In ji Davido.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG