Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabalenka Ta Sake Lashe Gasar Australian Open


Aryna Sabalenka
Aryna Sabalenka

Ita ce mace ta farko da ta sake lashe kofin gasar sau biyu a jere tun bayan Victoria Azarenka da ta cimma hakan a shekarar 2013.

‘Yar wasan Tennis ‘yar kasar Belarus Aryna Sabalenka ta lashe kofin gasar Australian Open na ajin mata, bayan da ta doke abokiyar karawarta ta kasar China Zheng Qinwen da ci 6-3- da 6-2 a yau Asabar.

Da ma dai Sabalenka mai shekaru 25, ita take rike da kofin gasar ta Austrilan Open, ta kuma kai wasan karshe ne bayan da ta doke ‘yar wasan Amurka Coco Gauf.

Ita ce mace ta farko da ta sake lashe kofin gasar a jere tun bayan Victoria Azarenka da ta cimma hakan a shekarar 2013.

Yanzu Sabalenka ta dauki hanyar shiga ajin fitattun ‘yan wasan Tennis irinsu Ash Baty, Serena Williams, Maria Sharapova da Lindsay Davenport.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG