Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN MURYAR AMURKA: Matakan Da Suka Dace Don Kawo Zaman Lafiya Da Tsaro A Haiti


FILE PHOTO: Haiti's National Penitentiary on fire, in Port-au-Prince
FILE PHOTO: Haiti's National Penitentiary on fire, in Port-au-Prince

Rikicin siyasa da karuwar tashe-tashen hankula a Haiti sun haifar da yanayi mai wahalar magancewa ga al'ummar Haiti.

"Ana buƙatar daukar matakin gaggawa a bangaren siyasa da tsaro don taimakawa wajen saita al’amura, don taimakawa al’umar Haiti."

"Muna goyon bayan shirin samar da wata hukumar shugabanci mai zaman kanta wacce da farko, za ta dauki kwararan matakai don biyan bukatun jama'ar Haiti."

"Na biyu, hukumsr ta ba da damar tura dakarun hadin gwiwa na wanzar da zaman lafiya.

“Na uku kuma, ta hanyar tura sojojin, ta hanyar taimakawa ‘yan sandan kasar Haiti, su samar da yanayin tsaron da ya dace don gudanar da zabe na gaskiya da adalci, don ba da damar kai taimakon jin kai ga mutanen da suke bukata, da kuma taimakawa wajen mayar da Haiti kan hanyar samun damar bunkasa tattalin arziki.”

Bisa la'akari da bukatar gaggawa da ake da ita a Haiti, Ma'aikatar Tsaro ta Amurka za ta ninka tallafinta zuwa dala miliyan 200 don dakarun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa don Haiti.

Kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka za ta kara dala miliyan 33 don taimakon jin kai.

"Mutanen Haiti ne kadai za su iya tantance makomarsu - ba kowa ba."

"Amma ... zamu iya taimakawa."

"Za mu iya taimakawa wajen maido da tsaro wanda zai iya magance wahalar da mutanen Haiti da ba su ji ba ba su gani ba ke fuskanta da kuma taimakawa wajen samar da yanayin da zai taimaka musu samun wannan damar."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG