Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gudun Hijirar Rohingya Da Dama Aka Ceto Daga Jirgin Ruwa Da Ya Kife Cikin Teku


APTOPIX Indonesia - Rohingya Muslims
APTOPIX Indonesia - Rohingya Muslims

A ranar Alhamis ne wani jirgin ruwa na kasar Indonesiya ya gano wani kwale-kwalen katako da ya kife da ‘yan gudun hijira Musulman Rohingya da dama, suka kuma ceto wadanda suka tsira da rayukansu da ke tsaye a kan katakon jirgin.

WASHINGTON, D. C. - Wani mai daukar hoto na kamfanin AP da ke cikin jirgin ceton ya ce an dauko mutane 10 a cikin kwale-kwale na kamun kifi na cikin gida sannan wasu 59 kuma jirgin na Indonesia ya ceto su.

Indonesia - Rohingya Muslims
Indonesia - Rohingya Muslims

Maza, mata da kananan yara, raunana da suke ake jike shataf saboda ruwan sama cikin dare, suna ta kuka a lokacin da aka fara aikin ceto, kuma an dauke mutane a cikin wani jirgin ruwan roba zuwa jirgin ruwan ceto.

Ba a dai san adadin 'yan gudun hijirar dake cikin wannan karamin jirgin ruwan ba a lokacin da ya kife a gabar tekun arewacin Indonesia a ranar Laraba, inda mutane shida da aka ceto da farko suka yi kiyasin mutane 60 zuwa 100 ne.

Babu tabbas ko duka sun yi nasarar manne wa jirgin da ya kife cikin dare ko kuma wasu sun nutse.

Rohingya Muslims
Rohingya Muslims

Tawagar aikin nema da ceto na Indonesiya sun bar birnin Banda Aceh ne kawai da yammacin Laraba, sa'o'i da yawa bayan kifewar jirgin, kuma da farko sun sha wahala wajen gano jirgin a cikin ruwan da ke gabar teku.

A karshe suka gano jirgin da wadanda suka tsira da tsakar ranar Alhamis.

Amiruddin, shugaban masu kamun kifi a gundumar Aceh Barat, ya ce wadanda aka ceto sun nuna cewa kwale-kwalen na tafiya gabas ne a lokacin da ya fara bulbulo da ruwa cikinsa, sannan karfin ta tura shi zuwa yammacin Aceh. Mutanen shida sun ce wasu na ci gaba da kokarin tsira a kan jirgin da ya kife.

Wani kwale-kwale da ya dauko Musulmai ‘yan Rohingya
Wani kwale-kwale da ya dauko Musulmai ‘yan Rohingya

Kimanin ‘yan kabilar Rohingya 740,000 ne dai aka musu matsugunai a kasar Bangaladesh domin gujewa mummunan yakin da jami’an tsaro ke yi a kasarsu ta Myanmar.

Dubban mutane ne ke kokarin tserewa cunkoson sansanoni a Bangladesh zuwa kasashe makwabta inda Indonesia ta ga karuwar ‘yan gudun hijira tun a watan Nuwamba wanda ya sa ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka. 'Yan Rohingya da suka isa Aceh na fuskantar wani kiyayya daga wasu 'yan uwa Musulmi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG