Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Za Su Tuhumi Tsohon Shugabar Brazil Kan Yin Jabun Takardar Shaidar Rigakafinsa Na COVID


Tsohon shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro
Tsohon shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro

‘Yan sandan Brazil sun ba da shawarar a tuhumi tsohon shugaban kasar, Jair Bolsonaro, kan zargin yin jabun takardar shaidar rigakafinsa na Covid, a cewar wani rahoton bincike da aka buga ranar Talata.

Tun bara ake ta gudanar da bincike kan Bolsonaro kan zargin cewa ya na shirin jirgita bayanan rigakafinsa na Covid a lokacin da ya ke shugabancin kasar inda ya sha suka saboda yin watsi da tsananin yaduwar cutar.

A cikin wani rahoto mai shafuka 231, rundunar ‘yan sandan tarayya ta ce Bolsonaro da wasu mutane takwas sun yi yinkurin gabatar da “takardun shaida na karya don samun fa’idar da ba ta dace ba” yayin barkewar cutar.

Yanzu ya rage ga ofishin babban mai shigar da kara ya yanke hukunci ko zai tuhumi Bolsonaro a wannan shari’ar.

Bolsonaro mai shekaru 68 da haihuwa ya fuskanci tambayoyi daga 'yan sanda kan zargin a watan Mayun bara, kuma an kai samame gidansa.

Ya musanta zarge-zargen kuma ya zargi hukumomi da kokarin yin masa kage.

Brazil Bolsonaro
Brazil Bolsonaro

Ofishin Kwanturola Janar na Brazil a watan Janairu ya tabbatar da cewa takardar shaidar Bolsonaro ta Covid jabu ce, amma ya ba da shawarar tsai da karar saboda "rashin isasshiyar shaida" kan wanda ya shigar da bayanan na karya.

Bolsonaro ya sha suka mai tsanani game da yadda ya tinkari annobar, bayan ya yi adawa da matakan takaita zirga-zirga.

Sannan a cikin raha ya ce maganin zai iya "maida mutum kada." Fiye da mutane 700,000 ne suka mutu sanadiyyar Covid a Brazil.

Bolsonaro ya kuma fadi cewa ba a yi masa allurar rigakafin ba.

Bayanan lafiyar jama'a sun nuna cewa ya karbi allurar rigakafin a Sao Paulo a watan Yuli 2022, amma ofishin kwanturolan ya gano cewa an shigar da bayan ta hanyar karya ne.

Ana kuma bincikensa kan zargin karkatar da wasu kyaututtuka da aka samu daga wasu kasashe kamar kayan kyalkyali da Saudiyya ta bayar.

An kuma dakatar da Bolsonaro daga rike mukamin gwamnati har zuwa shekarar 2030 saboda sukar da ya yi ta yi kan tsarin zabe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG