Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta’adda Sun Kai Mummunan Hari A Kan Gidaje Da Ke Bakin Wani Tashar Jiragen Ruwa Mallakar Kasar China


Gadar Gwadar, Pakistan
Gadar Gwadar, Pakistan

Hukumomi a Pakistan sun ce a ranar Laraba mutane 6 galibi jami'an tsaro ne suka mutu a lokacin da wasu gungun 'yan ta'adda dauke da muggan makamai suka kai hari a wani ginin gwamnati a birnin Gwadar da ke kudu maso yammacin kasar, garin da ke da wata tashar jiragen ruwa mallakar kasar China.

Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar da asarar rayuka, inda ya shaidawa Muryar Amurka cewa, dakarun Pakistan sun “yi gaggawar shiga tsakani” inda suka kashe “dukkan mahara takwas” a wani kazamin musayar wuta da suka yi.

Jami’in ya yi magana ne bisa sharadin sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai. Daga baya rundunar sojin Pakistan ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojoji biyu na daga cikin wadanda aka kashe a harin da mayakan suka kai.

Ta kara da cewa "an kuma samu nasarar kwato makamai da alburusai da ababen fashewa da dama daga hannun 'yan ta'addan da aka kashe."

Rundunar ‘yan sandan Baloch da aka haramta, ko BLA, ta dauki alhakin kai harin da yammacin ranar a harabar tashar jirgin ruwa ta Gwadar, wanda ke da ofisoshin farar hula da na tsaro.

A cikin wata sanarwa da ta aike wa manema labarai, kungiyar da Amurka ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci ta duniya, ta yi ikirarin cewa wani daga cikin ‘yan kungiyar da ta kira ‘yan kunar bakin wake, Majeed Brigade ne ya kai harin. Bai ba da wani ƙarin bayani ba. Jami'in tsaron ya shaidawa Muryar Amurka cewa, "Harin ya fara ne tare da wani bam da aka saka a cikin mota, amma bai samu tashi ba,".

Daga baya ‘yan ta’addan dauke da “bam-bamai, na’urorin harba roka, da manyan bindigu masu sarrafa kansu sun kai farmaki ginin, amma an kashe su yayin da aka maida martani.” Mazauna yankin da shaidun gani da ido sun ba da rahoton fashewar wasu bama-bamai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG