Matakin da Hukumar ta CSC ta dauka ya hada da bada umarnin dakatar da sake yada rahoton nan take tare da dakatar da shirye-shirye kafafen yada labaran kasa da kasar 2 tsawon makonni 2.
Amurka na shirin janye wasu dakarunta na wucin gadi daga kasar Chadi, a cewar jami'an Amurka a ranar Alhamis, matakin da ya zo kwanaki kadan bayan da Washington ta amince da janye sojojinta daga makwabciyarta Nijar.
Ambaliyar ruwa a Tanzaniya sakamakon ruwan sama da aka kwashe makonni ana yi ta yi sanadiyar mutuwar mutum 155 tare da jikkata wasu fiye da 200,000, in ji Firaiministan a ranar Alhamis.
Cutar zazzabin cizon sauro har yanzu babban kalubale ne ga lafiyar jama'a a Kenya, kodayake, ana iya samun wasu ci gaba.
Ghana ta fado kasa daga jerin kasashe goma (10) mafiya karfin tattalin arzikin Afirka a wannan shekarar, wanda Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar yayin da Asusun ya yi hasashen habakar tattalin arzikin Ghana da kashi 2.8 cikin dari nan da ƙarshen 2024.
Kawo yanzu dai babu wani mataki na karshe kan ko dukkan sojojin Amurka za su fice daga Nijar da Chadi ko kuma a'a, kasashen Afirka biyu da ke da muhimmanci ga kokarin da sojoji ke yi na dakile kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel.
‘Yan cirani 21 ne suka mutu, wasu 23 kuma suka bace bayan da wani kwale-kwalen da ke dauke da mutane 77 ya kife a gabar tekun Djibouti, lamarin da shi ne na biyu cikin makonni biyu, kamar yadda hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar Talata.
Anjarwalla dai ya tsere daga Najeriya ne biyo bayan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na daidaita tsarin hada-hadar kudi a wani yunkuri na karfafa darajar Naira.
Masana da kwararru sunyi nazarin cewa kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, na bukatar sake tsari da sauye-sauyen da za su yi daidai da manufofin kasashe mambobinta.
Gwamnatin mulkin soji a Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa uku bisa zarginsu da yin zagon kasa, kamar yadda wata takarda da gwamnati ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce ranar Alhamis.
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi wa fursunoni sama da 4,000 afuwa, ciki har da wasu da ke jiran hukuncin kisa, a wata afuwar zagayowar ranar bikin ‘yancin kai a ranar Alhamis.
Jirgin mai saukar ungulu na dauke ne da mutum 11 ciki har da Janar Ogolla a lokacin da ya fado kasa ya kama da wuta a kusa da kan iyakar kasar da Uganda.
Domin Kari
No media source currently available