Najeriya ta samu jarin dalar Amurka miliyan 600 na samar da kayayyakin aiki a tashar jiragen ruwa daga kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Denmark A.P. Moller-Maersk MAERSKb.CO, kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar ranar Lahadi.
Akalla jami'an rundunar sa-kai ta Civilian JTF ashirin da uku aka kashe a Najeriya a ranar Asabar a wasu hare-hare biyu da mayaka da ‘yan bindiga masu satar mutane suka kai a arewacin kasar.
Fubara ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gane wa idonsa da ya kai East-West Road da lamarin ya faru a daren Juma’a inda wata tankar mai ta kama da wuta ta halaka mutane tare da barnata dukiyoyi da dama.
Jim kadan bayan kamalla wani babban taro na musamman a kan yaki da ayyukan ta’adanci a nahiyar Afrika, kasashen nahiyar baki daya sun ce sun shirya tsaf don fitar da sabbin dabarun bai daya na yaki da matsalolin tsaro a matakin shiyya, tare da goyon bayan wasu kungiyoyin kasashen Turai kamar EU.
Bayanai sun yi nuni da cewa bayan da tankar ta kama da wuta, ta shafi motoci akalla goma da ke jerin cunkoson ababen hawa a birnin na Fatakwal.
sanarwar da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar tace, an warware matsalar.
Lamarin ya faru ne inda mamacin, wanda Manjo ne a rundunar sojin Najeriya, ke amsa kiran gaggawa na gudanar da aikin tsaro.
Hukumar FCCPC mai kare hakkin masu sayen kayayyaki a Najeriya tace masu ruwa da tsaki zasu sake nazari akan karin farashin baya-bayan nan da kamfanin Multichoice mai yada shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan adam yayi, domin tabbatar da cewar bai ha’inci abokan huldarsa dake Najeriya ba.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a wani shirin tashar talabijin ta Channels na jiya alhamis mai taken “Politics Today” a turance.
Rahotanni daga kaffafen yada labaran cikin gida na cewa akalla mutane 11 ne aka samo a karkashin baraguzan ginin da ake kan ginawa.
Daruruwan mazauna yankin Alawa ta karamar hukumar Shiroro a jihar Nejan Najeriya na ci gaba da tserewa daga gidajensu a sakamakon yadda mayakan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kai musu hare-hare.
Domin Kari
No media source currently available