Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Doke Angola A Gasar AFCON


Ivory Coast AFCON Soccer
Ivory Coast AFCON Soccer

Najeriya ta doke Angola ci 1-o a wasar Kwatal final na gasar AFCON da aka fafata a filin wasa na Félix Houphouët Biogny da ke Abidjan.

Ademola Lookman ne ya zura wa Najeriya kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ademola Lookman, wadda ya ke buga kungiyar kwallon kafar Atalanta, a kasar Italiya, ya farke a miniti na 41 da buga wasan.

Wannan nasara za ta ba wa Najeriya daman kai wa zagayen kusa da karshe a gasar, a karon farko cikin shekaru biyar.

Super Eagles dai ta fara gasar AFCON da kyar, inda ta yi kunnen doki da Equatorial Guinea kafin ta samu nasara a kan Cote d’Ivoire mai masaukin baki sannan kuma Guinea-Bissau. Tawagar ta Super Eagle ta kai zagayen gaba da maki bakwai.

A wasanta na zagaye na biyu, Najeriya ta doke abokiyar hamayyarta Kamaru da ci 2-0 inda ta sami dama shiga zagaye na gaba don karawa da kasar Angola.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG