Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Rasha Game Da Aniyar ISIS Ta Kai Hari Kasar


Amurka ta gargadi Rasha akan cewar mayakan kungiyar ISIS nada niyar kai hare-hare cikin kasar 'yan kwanaki gabanin maharan su afkawa gidan rawa na "Crocus City Hall" a wani hari da yayi sanadiyar mutuwar gwamman mutane saidai Shugaba Vladimir Putin yayi watsi da shawarar a matsayin "takalar fada".

WASHINGTON DC - A jiya Juma'a ne 'yan bindiga suka afkawa wani gidan rawa dake kusa da birnin Moscow, inda suka bude wuta tare da jefa abubuwa masu fashewa a harin ta'addancin mafi muni da aka taba kaiwa babban birnin Rasha a tsawon shekaru.

Tuni dai kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.

A farkon watan da muke ciki ne, ofishin jakadancin Amurka dake Rasha yace yana nazarin rahotannin dake cewar masu tsattsauran ra'ayi nada shirin afkawa dandazon mutane a birnin Moscow, ciki harda gidajen rawa sa'annan ta gargadi Amurkawa su kaucewa irin wadannan wuraren.

Kakakin Majalisar Tsaron Amurka, Andrienne Watson yace gwamnatin Amurka tayi musayar wannan bayani da hukumomin rasha a bisa dacewa da dadaddiyar manufar nan ta "hakkin yin gargadi".

Saidai a jawabin daya gabatar a Talatar data gabata, Shugaba Putin yayi fatali da gargadin na Amurka a matsayin takalar fada inda yace matakin yayi kama da kokarin bata suna da yin barazana da haddasa rudani a tsakanin al'umma.

Za'a iya cewar Rasha ta taka rawa ta zahiri a yakin basasar kasar Syria, inda ta goyi bayan Shugaba Bashar al-Asad akan kungiyar ISIS.

A jiya Juma'a, sakamakon rahotanni kaiwa gidan rawa na "Crocus City Hall" ofishin jakadancin Amurka dake Moscow ya gargadi Amurkawa akan yin balaguro zuwa Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG