Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Karin Mutane Biyar A Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna


Mutanen da 'Yan Bindiga suka saki daga cikin fasinjojin jirgan kasar Kaduna-Abuja.
Mutanen da 'Yan Bindiga suka saki daga cikin fasinjojin jirgan kasar Kaduna-Abuja.

Bayan kwashe sama da watanni hudu a daji, 'yan-bindigan da su ka sace mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun kuma sake sakin wasu mutane biyar cikin fasinjojin da ke hannun su.

Tun bayan sace fasinjojin jirgin kasan dai mutane sha dayan farko da aka sako ne kawai aka ce gwamnati ta shiga tsakani inda daga baya kuma tattaunawa ta koma tsakanin 'yan bindigan da kuma mutanen da su ka sace musu ‘yan uwa.

An saki mutane bakwai daga baya kuma aka kara sakin wasu mutane uku sai kuma gashi a jiya Talata 'yan bindigan sun sake sakin mutane biyar. Malam Mohammed Al'amin na cikin wadanda 'yan bindigan su ka sako kuma shine aka harba lokachin ya na hannun 'yan bindigan.

Mutanen da 'Yan Bindiga suka saki daga cikin fasinjojin jirgan kasar Kaduna-Abuja
Mutanen da 'Yan Bindiga suka saki daga cikin fasinjojin jirgan kasar Kaduna-Abuja

Al'Amin ya ce har yanzu ba shi da tabbas cewa ko harsashin da aka harbe shi ya na jikin shi ko kuwa ya fita saboda haka ya ce zai wuce asibiti ne don a duba halin da ya ke ciki. Ya ce sun shiga matsananchin hali saboda haka akwai bukatar ceto sauran mutanen da su ka rage a hannun 'yan bindigan.

Ganin mutanen da aka sako sun fara da zuwa ofishin mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu alhalin ya ce ba zai sake shiga tsakani ba ya sa shi bayanin cewa sun zo ne su yi mai godiya tare da rokon ya ci gaba da shiga tsakanin su da 'yan bindigan don ceto sauran mutanen da ke daji.

Ganin yadda matsalar tsaro ta yi tsanani ya sa masani kan harkokin tsaro, Dakta Yahuza Ahmed Getso nunawa gwamnati cewa sai ta jajirce tare da kara sojoji da kuma hukunta masu laifi kafin kawo karshen matsalar tsaro.

Sama da mutane 60 ne dai 'yan bindigan su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna kuma har yanzu mutane 28 ne kawai su ka tsira.

Ga rahoton Isah Lawal Ikara, Muryar Amurka daga Kaduna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG