Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chiefs Ta Yi Galaba Akan 49ers A Gasar Kwallon Zari Ruga Ta Super Bowl


NFL - Super Bowl LVIII - Kansas City Chiefs v San Francisco 49ers
NFL - Super Bowl LVIII - Kansas City Chiefs v San Francisco 49ers

A karon farko cikin shekaru 19 a gasar kwallon zari ruga ta NFL an samu kungiyar data sake maimaita nasara.

Kungiyar Chiefs ta birnin Kansas; wacce ta samu nasara har sau uku (3) cikin kaka biyar (5) ta sake tabbatar da matsayinta na daular zamani a gasar inda ta doke abokiyar karawarta San Francisco 49ers da ci 25 da 22 a filin wasa na Allegiant dake birnin Las Vegas a lahadin data wuce.

A wannan karon, kamar yadda kungiyar ta Birnin Kansas da mai tsaron bayanta Patrick Mahomes suka yi gasoshin biyu (2) da suka yi a baya, sun dawo da karfinsu a zagaye na biyu (2) na gasar-kuma a wannan karon suka nuna bajintar da aka jima ba’a ga irinta ba.

Kwallon da Jake Moody ya zura daga yadi na 27 bayan da suka mamaye wasan a zagayen farko tasa 49ers ta bada tazarar maki 22 da 19, saidai a martanin da Chiefs suka mayar da suka hada da bajinta 13, da wata dokawa daga tazarar yadi 75 wacce ta basu nasarar ajiye kwallon a yadi na 3 sakamakon cillata da Mecole Hardman ya yiwa Mahomes.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG