Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Mutane 20 Sun Mutu A Wani Kwale-kwale Da Ya Nutse A Gabar Tekun Senegal


Kwale-kwale Da Ya Nutse A Gabar Tekun Senegal
Kwale-kwale Da Ya Nutse A Gabar Tekun Senegal

Masu aikin ceto sun zakulo gawarwaki fiye da 20 daga tekun arewacin Senegal a ranar Laraba bayan da wani kwale-kwalen da ke dauke da bakin haure da ke kan hanyar zuwa Turai ya nutse, kamar yadda wani gwamnan yankin ya shaida wa AFP.

Gwamnan yankin Saint-Louis Alioune Badara Samb ya fadi ta wayar tarho cewa, “An gano gawarwaki sama da 20,” ya kuma kara da cewa an kuma ceto wasu karin mutane 20.

Badara Samb bai bayyana adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba amma wadanda suka tsira sun shaidawa AFP cewa adadin ya kai dari.

Mamady Dianfo, wanda ya fito daga Casamance da ke kudancin kasar mai nisa, ya ce akwai fasinjoji kusan 300 a lokacin da kwale-kwalen ya tashi daga Senegal mako daya da ya wuce.

Gaɓar tekun Senegal dai wani wuri ne da ake kara samun fitowar bakin haure 'yan Afirka da ke zuwa tsibirin Canary na Spain, tashar jiragen ruwa na shiga Turai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG