Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Ta Katse Huldar Soji Da Amurka


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.

Sanarwar da kakakin majalisar CNSP, Kanal Abdourahamane Amadou, ya gabatar a kafar talabijin mallakar gwamnati a cikin daren jiya Asabar na cewa Jamhuriyar Nijar ta tsinke huldar ayyukan soja da kasar Amurka sakamakon rashin gamsuwa da halaccin yarjejeniyar da aka fake da ita don shigo da dakarun sojan Amurka a kasar ta Nijar a 2012 cikin wani yanayi mai kama da tilashi ba dan rai ya so ba.

Haka kuma rashin samun wata gudunmowar da ta dace daga Amurka a yunkurin murkushe matsalolin tsaron da ke sanadin rasa rayukan sojoji da al’ummar Nijar ya sa majalisar CNSP da gwamnatin rikon kwarya suka umurci dakarun nan 1100 da Amurkar ta girke a sansanoni daban daban su fice daga wannan kasa ba tare da bata lokaci ba a cewar wannan sanarwa.

Wannan sabon al’amari na zuwa ne a washegarin rangadin da wata tawagar jami’an gwamantin Amurka ta gudanar a Nijar a karkashin jagorancin mataimakiyar sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harakokin Afrika, Molly Phee, inda suka tattauna da Fira Minista Ali Lamine Zeine da wasu mukarraban gwamnatinsa dangane da shirin mayar da Nijar tafarkin dimokradiya bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 koda yake yunkurin ganawar Amurkawan da Janar Abdourahamane Tiani ya ci tura, lamarin da ke fayyace alamun an yi watsewar baram baran a zaman da ya hada jami’an kasashen biyu.

A wani bangare na wannan sanarwa hukumomin na Nijer sun nuna rashin gamsuwa da abinda suka kira muguwar halayyar da sakatariya Molly Phee ta nuna a yayin ziyarar ta ranakun Talata, Laraba da Alhamis din da suka gabata.

Hulda a tsakanin Nijar da kasashen Russia da Iran na daga cikin batutuwan da sanarwar ta hukumomin mulkin sojan Nijar ta tabo, suna masu kare matsayin kasar da suka ce ta na da ‘yancin zabin kawayen da suka dace da manufofinta a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

Kasar Amurka wace ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023 ta dakatar da bai wa Nijar tallafin da ta saba bayarwa a fannoni da dama, ciki har da fannin tsaro. haka kuma ta sha yin hannunka mai sanda kan dukkan wani yunkurin kulla mu’amula da kasashe irinsu Rasha masu amfani da sojan haya a matsayin hanyar kula da sha’anin tsaro.

Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG