Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Peseiro Ya Yi Murabus Daga Matsayin Kocin Tawagar Super Eagles


Jose Peseiro
Jose Peseiro

Jose Peserio ya sanar da gama aikinsa na horar da 'yan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya bayan tawagar ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a kasar Ivory Coast.

Masaukin bakin gasar, Ivory Coast ce ta ci Najeriya a wasan karshe na gasar.

An ruwaito cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta NFF na tattaunawa kan sabunta kwantiragin kocin da ta kawo karshe a watan Fabrairun da ta gabata.

Peseiro ya ce "a jiya muka kawo ƙarshen kwantiragin da ke tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Najeriya NFF.

"Abin farin ciki da alfahari ne koyar da tawagar Super Eagles. Watanni 22 kenan da muka kwashe muna wannan sadaukarwa da matukar sha'awar aikin. Muna jin mun yi abin da ya kamata," kamar yadda kocin ya wallafa a shafinsa na X.

Peseiro ya nuna godiya ga shugabanin hukumar NFF na baya-bayanan da mai ci wato Amaju Pinnick da Ibrahim Gusau, Babban Sakataren Hukumar, Mohammed Sanusi da Sakatare Dayo Enebi.

Ya kuma nuna godiyarsa ga ‘yan wasa da ma’aikatan tawagar da suka mara masa baya a watani 22 da ya horar da 'yan wasan tawagar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG