Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soke Lasisin Dubban Kamfanonnin Canji Ba Zai Kawo Masalaha Ba ~ 'Yan Canji


Faduwar darajar Naira
Faduwar darajar Naira

'Yan kasuwar canjin kudi da dama sun nuna rashin gamsuwa da soke lasisin sama da kamfanonin canji 4000 da babban bankin Najeriya CBN ya yi.


Matakin dai ya kara jawo korafi daga masu canjin da ke cikin barazanar fuskantar samamen jami'an tsaro da ke zargin su da tada farashin dala.

Duk da daukar matakin yajin aiki na wuni daya da kasuwar canjin ta yi don barranta kanta da hannu a tashin farashin, hakan bai hana karin matakai masu tsauri kan 'yan canjin ba.

Alhaji Sani Danmasanin Dogon Daji da ke cikin wadanda aka soke mu su lasisi, ya ce ya cika ka'idojin da su ka dace amma bai tsira daga dirar mikiyar babban bankin ba.

Alhaji Sani ya ce wannan abin da CBN yayi ya kamata ya tsaya yayi nazari ya sake dubawa, saboda mutane da yawa sun bi ka’idojin da babban bankin ya bayar, amma sunayensu bai fito ba a jerin sunayen da suka fitar.

Shugaban kungiyar kasuwar canji ta Abuja, Alhaji Abdullahi Abubakar Dauran, ya ce su na biyaiya ga matakan gwamnati, amma ba su da hannu ko kadan a tashin farashin "mu ko nawa dala ta kama za mu yi kasuwancin mu don in ta sauko ma mun fi samun riba."

Shi kuma shugaban 'yan arewa mazauna kudu, Ambasada Musa Sa'idu, ya ce ba batun canjin kudi ne ya jefa Najeriya cikin tsada ba; hakan na da nasaba da jibgin bashin da gwamnatin Tinubu ta gada.

Gwamnan babban bankin CBN Olayemi Cardoso, ya dawo da tsarin ba wa 'yan canji dala don daidaita farashin sabanin yanda tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele ya dakatar da hulda da 'yan canjin da zargin su da tallafawa almundahana da kungiyoyin ta'addanci.

Cardoso ya yi alwashin daukar matakan rage tashin farashi da yanzu ya ke fiye da kashi 29 cikin 100 a Najeriya zuwa kashi 21.4 cikin 100.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG