Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Doke Ghana Da Ci 2-1 A Wasan Sada Zumunci


Tsohon hoto: karawar Najeriya da Ghana a wasan cin kofin duniya a 2022 a Rasha
Tsohon hoto: karawar Najeriya da Ghana a wasan cin kofin duniya a 2022 a Rasha

Dan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci kwallon farko da bugun fenariti a minti na 38. A minti na 84 ne kuma Ademola Lookman ya zura tasa kwallon.

Yau ‘yan wasan Najeriya Super Eagles sun doke takwarorin wasansu na Black Stars a wani wasan sada zumunta a kasar Morocco.

Najeriya ta doke kasar ta Ghana ne da ci 2-1.

Dan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci kwallon farko da bugun fenariti a minti na 38.

A minti na 84 ne kuma Ademola Lookman ya zura tasa kwallon.

Ghana ta ci kwallonta ne da bugun fenariti ta hannun dan wasanta Jordan Ayewa gab da ana kusan tashi a wasan.

Daya daga cikin 'yan wasan Ghana ya samu jan kati.

Haduwar kasashen biyu na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON da aka yi a Ivory Coast wacce ta lashe kofin.

Najeriya ta kai wasan karshe a gasar yayin da aka cire Ghana tun a zagayen rukuni-rukuni, lamarin da ya yi sanadin korar mai horar da ‘yan wasan kasar.

'Yan wasan Najeriya suna murnar zura kwallo a ragar Ghana a wasan sada zumunci a kasar Morocco a ranar 22 ga watan Maris, 2024 (Hoto: Facebook/Super Eagles)
'Yan wasan Najeriya suna murnar zura kwallo a ragar Ghana a wasan sada zumunci a kasar Morocco a ranar 22 ga watan Maris, 2024 (Hoto: Facebook/Super Eagles)

Tarihi ya nuna sau 56 Najeriya da Ghana suka kara a fagen kwallon kafa a gasa daban-daban da wasannin sada zumunci.

Ghana ta doke Najeriya sau 25 yayin da ita kuma Najeriya ta doke ta sau 12.

Sauran wasannin an tashi ne babu ci tsakanin kasashen biyu wadanda makwabtan juna ne a yankin yammacin Afirka.

Haduwa ta karshe da suka ita ce a wasan cin kofin duniya a 2022 da aka yi a Rasha inda Ghana ta fitar da Najeriya daga gasar.

Fitaccen dan wasan Najeriya Victor Osimhen bai samu zuwa wasan ba saboda rauni da ya ji.

Kazalika Taiwo Awoniyi da Tyronne Ebeuhi da Gabriel Osho duk ba su samu halartar wasan na sada zumunci ba.

A bangaren Ghana, fitaccen dan wasan kasar Thomas Partey, shi ma bai samu zuwa wasan ba.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG