Svoboda | Graniru | BBC Russia | Golosameriki | Facebook

Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Iya Lissafi Ne Ya Sa Wasu Suke Cewa An Yi Cushe A Kasafin Kudin 2024 – Tinubu


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

A makon da ya gabata dan takarar Shugaban kasa a zaben 2023 karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi kira da a gudanar da binciken “gaggawa” kan zargin na Ningi.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce rashin ilimin lissafi ne ya sa wasu suke zargin cewa an yi cushe a kasafin kudin kasar na 2024.

Kasafin na Najeriya na bana ya tashi akan Naira tiriliyan 28.7.

Majalisar Dattawa ta shiga rudani a baya-bayan nan, a lokacin da Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya ya yi zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudin bana.

Kazalika ya yi korafi kan yadda aka raba kudaden da aka ba mambobin majalisar don yi wa mazabunsu aiki.

‘Yan majalisar ta Dattawa sun musanta wannan zargi, suka kuma dauki matakin dakatar da Ningi tsawon watanni uku daga majalisar bayan kada kuri’a.

“Wadanda suke cewa an yi cushe a kasafin, ba su fahimci lissafin ba kuma ba su bi diddigin abin da na gabatar ba - kasafin kudi” Tinubu ya ce yayin da yake buda bakin azumin watan Ramadana da shugabannin majalisar ta dattawa a fadarsa ta Aso Rock kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Abdul Ahmed Ningi (Hoto: Facebook/Abdul Ningi)
Sanata Abdul Ahmed Ningi (Hoto: Facebook/Abdul Ningi)

Rahotanni sun yi nuni da cewa Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya goyi bayan Ningi inda ya ce ana dakatar da shi ne saboda ya fadi gaskiya.

A makon da ya gabata dan takarar Shugaban kasa a zaben 2023 karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi kira da a gudanar da binciken “gaggawa” kan zargin na Ningi.

Kazalika dan takarar shugaban kasa karkashin lemar LP, Peter Obi shi ma ya yi kira da a gudanar da bincike baya ga kungiyoyi da ke fafutukar tabbatar da adalci irin su CISLAC da su ma suka bi sahu.

Cushe a kasafin kudi a Najeriya, batu ne da aka jima ana zargin ana yi inda a lokuta-lokuta ya kan zama abin ka-ce-na-ce a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG